Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta gargaɗi duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da hankali ko kawo cikas a wuraren tarukan da za a gudanar gabanin ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar, cewa zai fuskanci hukunci bisa doka.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Shugaba Tinubu zai kai ziyarar aiki ta farko a Jihar Jigawa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayun 2023.
Ana sa ran shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu ayyuka tare da halartar tarukan siyasa a jihar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Tijjani Murtala, ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa muhimman wurare a birnin Dutse domin tabbatar da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan ziyarar.
Ya ce jami’an rundunar ’yan sanda, sojoji, hukumar NSCDC da DSS za su haɗa kai wajen gudanar da aikin tabbatar da tsaro.
Murtala ya kuma gargaɗi masu aikata laifuka, musamman masu satar wayoyi da kuɗaɗe daga jama’a a wuraren taro, da sauran masu aikata ƙananan laifuka.
Sai dai kwamishinan ya ce kawo yanzu ba a gano wata babbar barazanar tsaro ba, inda ya buƙaci jama’a da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya yayin ziyarar.