Sunday, November 8, 2026
HomeLabaraiRundunar ’yan sandan Kano ta kaddamar da samame a dazukan Gwamna, Gomo...

Rundunar ’yan sandan Kano ta kaddamar da samame a dazukan Gwamna, Gomo da Falgore

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta gudanar da wani gagarumin samame a dajin Gwamna da dajin Gomo, har zuwa dajin Falgore da ke kan iyakar jihar Bauchi, domin fatattakar ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka daga maboyarsu.

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta gudanar da wani gagarumin samame a dajin Gwamna da dajin Gomo, har zuwa dajin Falgore da ke kan iyakar jihar Bauchi, domin fatattakar ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka daga maboyarsu.

Rundunar ta bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, a matsayin wani mataki na tabbatar da tsaro a jihar, musamman a wannan lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara.

A cewar sanarwar, aikin na da nufin gano tare da wargaza sansanonin masu aikata laifuka, da kuma tabbatar da tsaron manoma, ’yan kasuwa da matafiya da ke bin hanyar Kano zuwa Bauchi.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya jagoranci sa ido kan aikin, inda ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da irin wannan samame har sai ta kawar da dukkan maboyar masu laifi a cikin jihar da kewaye.

Ya ce rundunar na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara, tare da samar da yanayin da zai ba da damar gudanar da zaɓen 2027 cikin kwanciyar hankali.

Kwamishinan ya kuma gode wa al’ummomin da ke makwabtaka da dazukan bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar yayin gudanar da aikin.

Musamman ya yaba wa mazauna ƙauyen Marmara da ke ƙaramar hukumar Sumaila, bisa tarba da suka yi wa jami’an tsaron, inda suka ba su abinci da abin sha tare da yi musu addu’ar samun nasara wajen kare ƙasa.

A ƙarshe, rundunar ta buƙaci jama’a da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da sahihan bayanai kan duk wani mutum ko motsi da suke zargi, ta hanyar kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kiran lambobin gaggawa: 08032419754, 08123821575 da 09029292926.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments