Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire rajistar masu zaɓe 1,608,660 da ba su kammala aikin tantancewa da inganta bayanansu ba daga kundin rajistar masu zaɓe na wucin gadi.
Haka kuma, hukumar ta gano ma’aikata 54 a jihohi 10 da ake zargin suna da hannu wajen aikata maguɗin rajistar masu zaɓe, inda aka ce za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansu, ciki har da yiwuwar gurfanar da su a gaban kotu.
Bugu da ƙari, INEC ta cire bayanan mutane 873 da aka tabbatar sun rasu daga kundin rajistar, bayan samun korafe-korafe da ƙalubale kan bayanansu.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja, yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon binciken da hukumar ta gudanar kan kundin rajistar masu zaɓe.
Ya ce waɗannan matakai na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da sahihanci da amincin kundin rajistar masu zaɓe da kuma inganta tsarin zaɓe a Najeriya.