Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na neman rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya, yana mai cewa hakan na iya zama nauyi ga gwamnatinsa idan ya karɓi mulki.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce bai kamata shugaban ƙasa mai barin gado ya ciwo sabon bashi a kwanakin ƙarshe na mulkinsa ya ɗora wa wanda zai gaje shi nauyin biya ba.
Ya bayyana cewa cin bashi ba tare da bayyana cikakkun sharuɗɗa da illolinsa ga al’umma ba, na iya jefa Najeriya cikin matsalar tattalin arziki. Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin ɗaure hannun gwamnatin da za ta gaje ta da sabon nauyin bashi.
Atiku ya yi kira ga Bankin Duniya da kada ya amince da rancen a lokacin da aka tsara, yana mai cewa ya kamata ‘yan Najeriya su samu cikakken bayani kan sharuɗɗan rancen, haɗarinsa da yadda za a biya shi.
A cewarsa, an tsara gabatar da batun rancen domin amincewa a ranar 25 ga Mayun 2027, kwanaki huɗu kafin rantsar da sabon shugaban ƙasa. Atiku ya ce gwamnatinsa za ta fara aiki ranar 29 ga Mayun 2027, kuma ba za ta fara mulki da karɓar sabon bashi ba, sai dai da tsarin shugabanci nagari da kula da tattalin arziki.