Mataimakin ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar NDC, Mustapha Rabi’u Kwankwaso, ya yi barazanar maka Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a kotu idan bai janye kalaman da ya yi a kansa ba tare da neman afuwa ba.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a wata hira da ya yi da Hadiza Gabon a shirinta na tattaunawa, Dawakin-Tofa ya bayyana cewa babu inda tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, bai kai ɗansa Mustapha ba a faɗin duniya wajen gyaran hali.
Kwamishinan ya kuma yi iƙirarin cewa mahaifin Mustapha ya kafa cibiyar gyaran hali ta Kiru ne saboda ɗansa.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Mustapha ya musanta zarge-zargen, inda ya bayyana kalaman kwamishinan a matsayin ƙarya da kuma yunƙurin ɓata masa suna da na iyalinsa.
Mustapha ya ce a lokacin da mahaifinsa yake mulki kuma ya kafa cibiyar gyaran halin ta Kiru, shi yana Dubai, inda yake gudanar da harkokin karatu da kasuwanci. Ya ƙara da cewa mahaifinsa ya ba shi tarbiyyar dogaro da kai, wadda ta taimaka masa wajen gudanar da kasuwancinsa a yanzu.
Ya kuma bayyana cewa ya samu tarbiyya da ilimin boko da na addinin Musulunci, yana mai cewa nadin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi masa a matsayin kwamishina ya samo asali ne daga cancantarsa, ba wai saboda buƙatar gyara halinsa ba kamar yadda Dawakin-Tofa ya yi iƙirari.
A ƙarshe, Mustapha ya ba kwamishinan wa’adin awanni 48 da ya janye kalamansa tare da neman afuwarsa a bainar jama’a, yana mai cewa idan har bai yi hakan ba, zai shigar da ƙara a kotu.