Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya na shirin yi wa masu digiri daga kasashen waje jarabawar...

Gwamnatin tarayya na shirin yi wa masu digiri daga kasashen waje jarabawar tantancewa kafin NYSC

Gwamnatin Tarayya na nazarin yi wa ’yan Najeriya da suka kammala karatun digiri a jami’o’in ƙasashen waje jarabawar tantance ilimi kafin amincewa da takardun shaidar karatunsu da kuma ba su damar shiga shirin bautar ƙasa (NYSC).

Daraktar Yaɗa Labarai ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.

Sanarwar ta ce an gabatar da shawarar ne yayin taro na 37 na Kwamitin Tantance Takardun Shaidar Karatu daga Ƙasashen Waje, wanda aka gudanar a Abuja.

Darakta mai kula da Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar, Dakta Folake Olatunji-David, ce ta gabatar da shawarar, musamman ga waɗanda suka yi karatu a jami’o’in ƙasashen Afirka, domin tabbatar da cewa sun halarci jami’o’in da suka bayar da takardunsu tare da samun ilimin da ya dace.

Ta bayyana cewa karuwar ’yan Najeriya da ke neman ilimi a ƙasashen waje, musamman a Yammacin Afirka, ta sa ya zama wajibi a ƙarfafa tsarin tantance takardun karatu da kuma sahihancin jami’o’in da ke bayar da su.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa tun farkon shekarar 2026 ta mayar da tsarin tantance takardun karatu zuwa tsarin fasahar zamani, yayin da kwamitin ke ci gaba da nazarin wasu hanyoyin tabbatar da sahihancin takardun shaidar karatu daga ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments