Tuesday, November 10, 2026
HomeSiyasaMajalisar Kwankwasiyya ta ba Sanusi Bature wa’adin awanni 48 ya janye kalamansa...

Majalisar Kwankwasiyya ta ba Sanusi Bature wa’adin awanni 48 ya janye kalamansa kan Mustapha Kwankwaso

Majalisar Kwankwasiyya Concerned Council ta yi Allah-wadai da kalaman da ake zargin sabon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya yi kan Mustapha Rabi’u Kwankwaso, tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni kuma mataimakin ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, M. Saeed Kano, ya sanya wa hannu a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, majalisar ta bayyana rashin jin daɗinta da kuma Allah-wadai da kalaman, waɗanda ta ce ba su dace da matsayin wanda ke riƙe da muƙamin kwamishinan gwamnati ba.

Majalisar ta ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai an kafa ta ne domin sanar da al’umma manufofi, shirye-shirye da ayyukan gwamnati, don haka bai kamata a mayar da ita wajen yaɗa kalaman siyasa, kai hare-hare kan mutane ko ɓata sunan wasu ba.

A cikin buƙatunta, majalisar ta nemi Sanusi Bature ya janye kalaman da ta bayyana a matsayin marasa tushe, sannan ya fito fili ya nemi afuwar Mustapha Kwankwaso da iyalinsa.

Haka kuma, ta ba shi wa’adin awanni 48 daga ranar fitar da sanarwar domin ya bi waɗannan buƙatu, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin shari’a idan har ya ƙi yin hakan.

Majalisar ta jaddada cewa ba za ta ɗauki son zaman lafiya da siyasa cikin lumana a matsayin rauni ba, tana mai cewa bambancin siyasa bai kamata ya zama dalilin kai hare-haren mutumci ko amfani da muƙaman gwamnati wajen cimma wata manufa ta siyasa ba.

Ta kuma yi kira ga gwamnatin Kano da masu riƙe da muƙaman gwamnati da su mayar da hankali kan shugabanci nagari, riƙon amana da magance matsalolin da ke addabar al’ummar jihar.

@⁨Mah Role Model🥰💔⁩

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments