Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa Najeriya ce ke da kaso 25 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu da ake samu a faɗin duniya.
Ta kuma ce mace ɗaya cikin mata 22 a Najeriya na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon juna biyu ko haihuwa.
Wakiliyar UN Women a Najeriya da ECOWAS, Beatrice Eyong, ce ta bayyana hakan yayin taron shekara-shekara kan lafiyar mata da haƙƙoƙin haihuwa da aka gudanar a Abuja.
Ta buƙaci gwamnati da ƙungiyoyin ci gaba su magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da ke haddasa mace-macen, tare da inganta dokoki da kare haƙƙin mata.
Ministan Matasa, Olawande Ayodele, da Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, sun jaddada muhimmancin bai wa matasa da mata damar samun ingantattun bayanai da ayyukan kiwon lafiya, musamman wajen kula da masu juna biyu da jarirai.