’Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan matakin rage farashin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka, inda wasu ke ganin hakan tamkar dawo da tallafin man fetur ne a kaikaice, duk da cewa gwamnati ta musanta hakan.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki matakin, yana mai bayyana shi a matsayin dabarar siyasa da za ta samar da sauƙi na ɗan lokaci kawai.
Atiku, wanda ke shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya bayyana ra’ayinsa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin matakin ga tattalin arzikin ƙasar da rayuwar al’umma.
Sai dai gwamnatin Tinubu ta musanta cewa rage farashin man fetur ɗin na nufin dawo da tallafin mai, yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabambanta kan matakin.