Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC-PCC ya soki Shugaba Bola Tinubu kan rahotannin cewa ba zai gudanar da yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohin Najeriya ba gabanin zaɓen 2027, inda ya bayyana matakin a matsayin girman kai da raina ’yan Najeriya.
Kwamitin ya ce shugaban ƙasa da ke neman wa’adin mulki na biyu ya kamata ya kasance a shirye domin ganawa da masu zaɓe, bayyana nasarorin gwamnatinsa da kuma gamsar da ’yan Najeriya kan dalilin da ya sa ya kamata su sake zaɓensa.
Ya kuma yi iƙirarin cewa ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya ƙara wa ADC ƙarfin siyasa, yana mai cewa taron bai jawo goyon bayan ’yan ADC ko masu mara mata baya ba.
Darakta mai kula da yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar matasa ƙarƙashin ƙungiyar Young Voters for Atiku (YVA).
Ologbondiyan ya ce rahoton cewa Tinubu ba zai zagaya ƙasar domin yaƙin neman zaɓe ba zai iya bai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, wata dama, saboda a cewarsa, Atiku a shirye yake ya ziyarci dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin ganawa da ’yan ƙasa da bayyana manufofinsa.
Ya bayyana Atiku a matsayin wanda yake da kuzari a jiki da kuma ƙoshin lafiya a tunani, wanda a shirye yake ya gudanar da yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar.
“Abin da Shugaba Tinubu ya yi wani babban mataki ne na raina ’yan Najeriya. An san APC da raina ’yan Najeriya. Ta yaya mutumin da yake son a sake zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa, bayan ya gaza matuƙa, zai ce ba ya son ziyartar mutanen da yake neman ya mulka? Wannan ya saɓa wa al’ada,” in ji Ologbondiyan.
Mai magana da yawun ADC-PCC ya kuma ƙalubalanci hujjar cewa ayyukan gwamnati za su hana Tinubu gudanar da yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar.
Ya yi nuni da tsoffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, yana mai cewa sun ci gaba da gudanar da ayyukansu na gwamnati yayin da suke yaƙin neman zaɓen wa’adin mulki na biyu. Ya kuma ambaci Donald Trump da Kamala Harris na Amurka a matsayin misalan ’yan siyasar da suka gudanar da yaƙin neman zaɓe.
Ologbondiyan ya ƙara zargin shugaban ƙasar da ɗaukar ’yan Najeriya da wasa, yana mai cewa duk shugaban da ba ya son fuskantar masu zaɓe bai kamata ya nemi wa’adin mulki na biyu ba.
“Shugaba Tinubu ya ɗauki ’yan Najeriya a matsayin abin wasa, kuma bai kamata ya nemi sake tsayawa takara ba. Shugaban da yake tsoron fuskantar al’ummarsa ba shi da hurumin neman ƙuri’unsu,” in ji shi.
Ya ce neman sabon wa’adin mulki yana buƙatar tawali’u, riƙon amana da kuma shirye-shiryen amsa tambayoyin jama’a kan halin da ƙasar take ciki.
Darakta na ADC-PCC ya kuma yi zargin cewa rashin gamsuwar jama’a kan yunwa, talauci, rashin tsaro da matsalolin tattalin arziki na iya zama dalilin da ya sa ake cewa shugaban ƙasar ba ya son gudanar da yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohi.
Kwamitin ya yi kira ga ’yan Najeriya, musamman matasa, da su ƙi zaɓen APC a babban zaɓen 2027, yana mai cewa sake ba jam’iyyar mulki zai tsawaita wahalhalun da jama’a ke fuskanta.