Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan rangwamen Naira 66 a kan kowace litar fetur da kamfanin NNPC Limited ya sanar, yana mai cewa ba a samar da shi ga dukkan ’yan Najeriya ba.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya tambayi wanda zai ɗauki nauyin kuɗin rangwamen, da kuma ko hukumar gudanarwar NNPC ta amince da matakin kafin sanar da shi.
Atiku ya ce NNPC na da gidajen mai sama da 900 kacal a ƙasar da ke da kusan mutane miliyan 242, yana mai tambayar yadda waɗanda ke zaune nesa da gidajen man za su amfana da rangwamen.
Ya kuma yi tambaya kan halin masu ababen hawa da za su kashe kuɗin fetur da lokaci wajen zuwa gidajen man NNPC, su yi layi, sannan su yi amfani da manhaja domin samun rangwamen.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zargi Tinubu da mayar da rangwamen wani abin neman yabo na siyasa, yana mai cewa sauya sunan wani kuɗi zuwa rangwame ba ya kawar da ainihin kuɗin da za a kashe. Ya ce ’yan Najeriya na buƙatar fetur mai araha a faɗin ƙasar, ba rangwamen Naira 66 da sai an sha wahala kafin a samu ba.