Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMakinde ya bukaci ’yan Najeriya su tuna alkawarin Tinubu kan wutar lantarki...

Makinde ya bukaci ’yan Najeriya su tuna alkawarin Tinubu kan wutar lantarki kafin zaɓen 2027

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bukaci ’yan Najeriya su yi la’akari da alkawarin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalar wutar lantarki kafin su yanke shawarar wanda za su zaɓa a zaɓen 2027.

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bukaci ’yan Najeriya su yi la’akari da alkawarin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalar wutar lantarki kafin su yanke shawarar wanda za su zaɓa a zaɓen 2027.

Makinde, wanda yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APM, ya yi wannan kira ne a ranar Asabar yayin taron jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a Yola.

Ya tuna cewa Tinubu ya yi alkawarin gyara matsalar wutar lantarki a Najeriya cikin shekaru huɗu, yana mai cewa ya kamata ’yan Najeriya su yi la’akari da halin da fannin wutar lantarki yake ciki wajen zaɓen shugabanni.

A nasa jawabin, jagoran jam’iyyar APM na ƙasa kuma Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa mambobi da masu ruwa da tsaki kan goyon bayan da suka nuna wa Makinde, tare da bayyana jam’iyyar a matsayin dandalin siyasa da zai iya taimakawa wajen magance matsalolin Najeriya.

Mohammed ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su marawa jam’iyyar APM da ’yan takararta baya a babban zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments