Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwani da ya samar da Bashir Abdullahi Gaddafi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ADC mai wakiltar mazaɓar Akko a Majalisar Wakilai ta Tarayya a zaɓen 2027.
Mai shari’a Vera E. Ibrahim ce ta yanke hukuncin, tare da umartar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 21, sannan a janye takardar shaidar takararsa nan take.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Adamu Hassan Kashere ya shigar, yana zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani a rumfunan jam’iyyar da ke mazaɓar ba.
Sai dai kotun ta ce Kashere bai tabbatar da zargin cewa Gaddafi ya ci gaba da karɓar albashi a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati yayin takara ba. Ta kuma tabbatar da cewa Gaddafi ɗan jam’iyyar ADC ne mai cancantar shiga zaɓen fidda gwani.
Bayan yanke hukuncin, lauyoyin ɓangarorin biyu, Ibrahim Aliyu Nasarawa da Benjamin Sati, sun ce za su tuntubi waɗanda suke wakilta kafin yanke shawarar matakin da za su ɗauka na gaba.