A rana irin ta yau, 8 ga Oktoba, 1932, aka kafa Rundunar Sojin Saman Indiya (Indian Air Force) a lokacin da Indiya ke ƙarƙashin mulkin Daular Burtaniya.
A wancan lokaci, an kafa rundunar ne a matsayin wata runduna ta taimako ƙarƙashin tsarin sojin sama na Birtaniya, inda aka saka mata suna Royal Indian Air Force.
A farkon kafuwarta, rundunar ba ta da manyan kayan aiki. Ta fara ne da jiragen sama guda huɗu na samfurin Westland Wapiti, tare da matukan jirgi biyar da aka horar a ƙasar Ingila.
Bayan Indiya ta samu ’yancin kai a shekarar 1947, rundunar ta cire kalmar “Royal” daga sunanta, inda ta koma Indian Air Force (IAF).
Tun daga wannan lokaci, rundunar ta ci gaba da haɓaka ƙarfin sojinta ta hanyar mallakar sabbin jiragen sama da horar da ƙwararrun jami’ai.
A yau, Indian Air Force na daga cikin manyan rundunonin sojin sama a duniya, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen kare sararin samaniyar ƙasar.