Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiBwala: Sauye-sauyen Tinubu sun jefa ƙarin ’yan Najeriya cikin talauci

Bwala: Sauye-sauyen Tinubu sun jefa ƙarin ’yan Najeriya cikin talauci

Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsu ta aiwatar sun taimaka wajen ƙara yawan ’yan Najeriya da suka shiga cikin talauci, sai dai ya ce gwamnati ta samu gagarumar nasara tun bayan fara aiwatar da matakan.

Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsu ta aiwatar sun taimaka wajen ƙara yawan ’yan Najeriya da suka shiga cikin talauci, sai dai ya ce gwamnati ta samu gagarumar nasara tun bayan fara aiwatar da matakan.

Bwala ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels Television ranar Laraba, yayin da yake kare manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar tun bayan hawanta mulki a shekarar 2023.

Sauye-sauyen, musamman cire tallafin man fetur da na kasuwar canjin kuɗin waje, sun haifar da tashin farashi, yayin da farashin sufuri, jigilar kayayyaki da kuɗaɗen samar da kayayyaki suka ƙaru a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta sha nanata cewa matakan sun zama dole ne domin gyara matsalolin tattalin arzikin da suka daɗe suna addabar ƙasar tare da inganta matsayinta na kuɗi.

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana a jawabinsa na ranar 1 ga Oktoba, ranar samun ’yancin kai, cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu daga kololuwarta, ajiyar kuɗin waje ya inganta, yayin da kasuwar canjin kuɗin waje ta samu daidaito.

Bwala ya amince cewa sauye-sauyen sun jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, musamman waɗanda tuni suke fama da ƙarancin kuɗi.

“Ina so a fahimci wannan, har ma da ’yan adawa, cewa dalilin da ya sa kuke da wannan adadin talakawa da kuma wasu daga cikin alkaluman da ake bayarwa na cewa komai ya lalace, shi ne saboda mun aiwatar da sauye-sauye.”

Sai dai ya ce an samu nasara sosai domin irin wannan aikin gyara ya gaji haka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments