A ranar 8 ga Oktoba, 1871, wata babbar gobara ta tashi a birnin Chicago na ƙasar Amurka, wadda daga baya ta zama ɗaya daga cikin munanan gobara a tarihin birnin.
Gobarar ta tashi ne da daddare a wani wuri da ke kusa da gidan iyalan O’Leary. Saboda tsananin iska da kuma yawan gine-ginen katako da ke birnin a lokacin, wutar ta bazu cikin sauri, inda ta mamaye sassa da dama na Chicago.
Gobarar ta ci gaba da ruruwa na tsawon kwanaki biyu, har zuwa ranar 10 ga Oktoba. Ta lalata wani yanki mai faɗin kusan murabba’in kilomita 9, tare da kashe kusan mutane 300.
Haka kuma, sama da mutane 100,000 suka rasa matsugunansu sakamakon wannan bala’i, yayin da gidaje da gine-gine masu yawa suka kone kurmus.
Bayan gobarar, birnin Chicago ya fara wani gagarumin shiri na sake gina garin , inda aka samar da sabbin ƙa’idojin gine-gine da suka fi mai da hankali kan ƙarfi da kariya daga gobara.
Wannan sake ginawa ya taimaka wajen sauya fasalin Chicago, tare da mayar da birnin cikin manyan biranen zamani na Amurka.