Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin ɗaukar kwararan matakai na gaggawa domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, bayan hare-haren ’yan bindiga da suka shafi wasu ƙananan hukumomi huɗu na jihar.
Hare-haren sun shafi yankin Chiromawa da ke Ƙaramar Hukumar Garun Mallam, Beli a Ƙaramar Hukumar Rogo, Bebeji, da kuma wasu al’ummomi da ke kewayen Gwarzo.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya bayyana hare-haren a matsayin abin damuwa matuƙa da kuma lamarin da ba za a amince da shi ba.
Gwamnan ya jajanta wa waɗanda hare-haren suka shafa da iyalansu, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da hukumomin tsaro domin hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.
Ya ce an umarci hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen sa ido, tattara bayanan sirri da kuma inganta hanyoyin ɗaukar matakin gaggawa a yankunan da ke cikin haɗari.
Gwamna Abba ya kuma buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar matakan da ka iya ƙara dagula lamarin, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai.
Ya yi kira ga jama’a da su riƙa isar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimaka musu wajen dakile hare-hare da kuma cafke waɗanda ke da hannu a aikata laifukan.
Gwamnan ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi, inda ya buƙace su da su ci gaba da amfani da sahihan bayanan sirri wajen gudanar da ayyukan tsaro da kare al’ummomin da ke cikin haɗari.
Haka kuma, Gwamna Abba ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya, sannan Ya dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su cikin aminci.
Ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.