Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu na sane da irin ƙuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki...

Tinubu na sane da irin ƙuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki – Gwamnan Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana sane da irin ƙuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Sule ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Lafia.

Gwamnan ya ce duk da cewa wasu muhimman alamomin tattalin arzikin ƙasar na nuna samun sauƙi, har yanzu tasirin wannan sauƙin bai kai ga talakawa da sauran ‘yan Najeriya yadda ya kamata ba.

A cewar Sule, Shugaba Tinubu ya fahimci wannan ƙalubale, kuma ya buƙaci gwamnonin jihohi da su ƙara mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da za su sauƙaƙa rayuwar jama’a.

Ya ce daga cikin abubuwan da shugaban ƙasar ya umarci gwamnonin su mayar da hankali a kansu akwai gina hanyoyin karkara, samar da ruwan sha, wutar lantarki da kuma shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arzikin jama’a.

Sule ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka za su taimaka wajen inganta rayuwar mazauna karkara tare da samar musu da damar bunƙasa harkokin noma da sauran sana’o’insu.

Gwamnan ya kuma yi nuni da cewa duk da ƙarin asusun ajiyar kuɗin waje na Najeriya daga ƙasa da dala biliyan 30 zuwa sama da dala biliyan 50, wannan ci gaban bai isa ya zama abin jin daɗi ga talakawa ba matuƙar ba su fara ganin sauyin a rayuwarsu ba.

Ya ce idan aka gaya wa wani mazaunin ƙauye cewa asusun ajiyar kuɗin waje ya haura dala biliyan 50, tambayar da zai iya yi ita ce: “Ta yaya wannan zai taimaka wajen inganta rayuwata?”

Gwamna Sule ya ce wannan na nuna muhimmancin mayar da hankali kan manufofin da za su sauya rayuwar jama’a kai tsaye, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments