Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaNDC: Aminu Warkal ya zargi shugaban jam’iyyar Kano Mairiga da cin amanarsa

NDC: Aminu Warkal ya zargi shugaban jam’iyyar Kano Mairiga da cin amanarsa

Hon. Aminu Abdullahi Warkal, ɗaya daga cikin ‘yan siyasar jam’iyyar NDC a Kano, ya zargi shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Hussaini Isa Mairiga, da cin amanarsa bayan da aka cire sunansa daga cikin jerin ‘yan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kano da za su wakilci Ƙaramar Hukumar Gwale.

Warkal ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce cire sunansa daga jerin ‘yan takarar ya zama masa cin amana.

Ya kuma zargi shugaban jam’iyyar na jihar da hannu wajen aika buƙatar cire sunansa daga jerin ‘yan takarar zuwa ofishin uwar jam’iyyar NDC na ƙasa.

A cewar Warkal, abin da ya faru ya sa ya ji an ci amanarsa, yana mai cewa zai bar lamarin a hannun Allah.

Warkal ya ce: “Da hannunsa ya ci amanar jagora, ya ci amanarmu. Shi ne ya rubuta wa ofishin uwar jam’iyyar NDC ta ƙasa a cire sunanmu.”

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi hukunci a tsakaninsa da shugaban jam’iyyar kan abin da ya ce an yi masa.

Sai dai har yanzu ba a samu martanin Hon. Hussaini Isa Mairiga kan waɗannan zarge-zargen ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments