Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran adawa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.
Kwankwaso, a cikin saƙonsa, ya bayyana Adeleke a matsayin abokinsa, yana mai cewa nasarar ta nuna muhimmancin ikon jama’a wajen tabbatar da zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.
Ya kuma yaba wa al’ummar Osun bisa yadda suka fito suka yi amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya, tare da kira ga ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da mutunta tsarin zaɓe mai inganci, gaskiya da zaman lafiya.
Kwankwaso ya kuma yaba wa INEC kan yadda ta gudanar da zaɓen, tare da taya Adeleke da al’ummar Osun murnar nasarar.