Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaTikitinmu da Peter Obi ba shi da hamayya a 2027 – Kwankwaso

Tikitinmu da Peter Obi ba shi da hamayya a 2027 – Kwankwaso

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa haɗin kansa da Peter Obi ya fi sauran tikitin takara ƙarfi wajen cancanta da ƙwarewar jagoranci a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kwankwaso ya ce haɗin kansu zai samu goyon bayan Obi daga Kudu tare da tasirinsa na siyasa a Arewa, abin da ya ce zai samar da tikitin da zai haɗa ’yan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko yanki ba.

Tsohon gwamnan Kano ya ce Najeriya na buƙatar sauyi domin tunkarar matsalolin tsaro, talauci da tabarbarewar ababen more rayuwa.

Ya ce ya amince da zama mataimakin Obi ne domin yi wa ƙasa hidima da kuma taimakawa wajen samar da sauyin dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments