Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro bisa gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun cikin lumana da gaskiya.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.
INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u 511,067.
Shugaban ya ce sakamakon zaɓen ya nuna ra’ayin al’ummar Osun, yana mai bayyana nasarar a matsayin wata alama da ke nuna cewa dimokuraɗiyya na ci gaba da bunƙasa a Najeriya.
Kafin zaɓen, Tinubu ya buƙaci INEC ta tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaɓen, sannan ya umarci jami’an tsaro da su kare masu zaɓe da jami’an INEC tare da tabbatar da zaman lafiya.