An buɗe gasar ‘kasa da kasa na gasar Al-Kur’ani mai tsarki na Sarki Abdulaziz karo na 46 a ranar Alhamis a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, inda aka samu mahalarta mafi yawa tun bayan fara gudanar da gasar.
Ana gudanar da gasar ne ƙarƙashin jagorancin Mai Kula da Masallatan Harami Biyu, Sarki Salman, yayin da Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci, Wa’azi da Shiryarwa ta Saudiyya ke shirya ta. Za a ci gaba da gasar har zuwa ranar 6 ga watan Rabi’ul Awwal, wadda ta yi daidai da ranar 19 ga watan Agusta.
Jimillar mahalarta maza da mata 334 daga ƙasashe 133 ne ke fafatawa a gasar bana, lamarin da ya sa ta zama mafi girma tun bayan ƙaddamar da ita.
Masu shirya gasar sun ce manufarta ita ce ƙarfafa matasa Musulmi su haddace Alƙur’ani Mai Girma, su fahimci ma’anoninsa tare da yin nazari a kansa, sannan ta bunƙasa gasa mai tsafta tsakanin mahalarta daga sassa daban-daban na duniya.
Sun kuma bayyana cewa gasar na nuna irin ƙoƙarin da Masarautar Saudiyya ke yi wajen hidima ga Alƙur’ani Mai Girma da kuma girmama masu haddace shi.
A wani tarihi na musamman, za a gudanar da gasar mata daban a Makkah Hilton Hotel & Convention a karon farko, yayin da za a gudanar da wasan ƙarshe na maza da bikin rufe gasar a Harami.
Gasar ta ƙunshi rukuni biyar, tare da jimillar kyautar riyal miliyan 10.26 na Saudiyya (kimanin N3.7bn), wadda ita ce mafi girma tun bayan fara gudanar da wannan gasa ta ƙasa da ƙasa.
Ana ɗaukar wannan gasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan gasannin Alƙur’ani mafi daraja a duniya, inda fitattun mahaddata da makaranta Alƙur’ani daga ƙasashe daban-daban ke halarta.