Fadar Shugaban Ƙasa ta kare manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓar bashi. Ta bayyana cewa manyan ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a jihohi daban-daban sun nuna cewa ana amfani da kuɗaɗen wajen bunƙasa ƙasa, ba almubazzaranci ba.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin rangadin duba ayyukan gwamnatin tarayya da aka gudanar a jihar Benue.
Rangadin, wanda ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors (RHA) ta shirya tare da haɗin gwiwar Presidential Media Team, ya nuna ayyukan gwamnatin tarayya da na jihar da ake aiwatarwa ƙarƙashin shirin gwamnati na inganta Najeriya.
Bayan duba gadar Buruku mai tsawon mita 854 da aka gina a kan kogin Katsina-Ala, Onanuga ya ce zuba jari da gwamnati ke yi a hanyoyi, gadoji da masana’antu ya zama amsa ga masu sukar yadda gwamnati ke karɓar bashi.
Ya ce:
“A matsayinmu na ‘yan Najeriya, muna ganin ana zargin gwamnati da karɓar bashi. Amma muna kuma ganin inda kuɗin ke tafiya; wajen bunƙasa ababen more rayuwa, tabbatar da kasuwanci yana tafiya cikin sauƙi da kuma bai wa manoma damar kai amfaninsu kai tsaye kasuwa.”
Onanuga ya bayyana cewa gadar Buruku na ɗaya daga cikin gadoji biyar da gwamnatin tarayya ke ginawa a jihar Benue, yana mai cewa za ta sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin jihohin Benue, Taraba da Adamawa tare da ƙarfafa harkokin tattalin arziki tsakanin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.
Ya ƙara da cewa:
“Wannan aiki zai amfani kowa ta fuskar tattalin arziki.”
Babban Daraktan Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya a Benue, Engr. Mukaila Danlandi, ya ce an fara aikin a shekarar 2023 kuma ana sa ran kammala shi zuwa watan Disambar 2027.
A cewarsa, an kammala dukkan manyan sassan ginin da ke ƙarƙashin gada, yayin da aka shirya girke manyan katakon gada bayan damina.
Danlandi ya ce:
“Babu wata matsalar kuɗi. Aikin na ƙarƙashin Asusun Renewed Hope Infrastructure Fund.”
Ya kuma ce matsalar biyan diyya da ta jinkirta aikin a baya ta warware ne da taimakon gwamnatin jihar Benue.