Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiMafi ƙarancin albashin 70,000 ba ya wadatar da ma’aikata a halin yanzu...

Mafi ƙarancin albashin 70,000 ba ya wadatar da ma’aikata a halin yanzu – NLC

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba mafi ƙarancin albashin ma’aikata na 70,000, suna masu cewa adadin ba zai iya biyan buƙatun rayuwar ma’aikata ba a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa hauhawar farashin abinci, sufuri, gidaje da sauran muhimman buƙatu ya sa albashin da ake biya a halin yanzu ya rasa ƙarfin da zai iya tallafa wa ma’aikaci da iyalansa.

A cewarsu, akwai buƙatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su sake nazarin tsarin albashi domin ya dace da halin tattalin arzikin ƙasar, tare da tabbatar da cewa ma’aikata na samun albashin da zai inganta rayuwarsu.

NLC ta jaddada cewa inganta walwalar ma’aikata na da matuƙar muhimmanci wajen ƙara ƙwazo da bunƙasa ayyukan gwamnati da ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments