Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwankwaso: lokaci ya yi da shugabanni za su ɗauki matakan rage wa...

Kwankwaso: lokaci ya yi da shugabanni za su ɗauki matakan rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin rayuwa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar manyan ƙalubale da suka haɗa da tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsin tattalin arziki, yana mai cewa lokaci ya yi da shugabanni za su ɗauki matakan gaggawa domin sauƙaƙa wa al’umma halin da suke ciki.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 4 ga Agustan 2026, Kwankwaso ya yabawa taron Limaman Cocin Katolika na Najeriya (CBCN), yana cewa sun nuna kishin ƙasa ta hanyar fito da damuwar da ta shafi rayuwar ’yan Najeriya.

Ya ce duk da dimbin albarkatun da ƙasar ke da su, har yanzu mutane da dama na fama da rashin aikin yi, matsin tattalin arziki, ƙarancin ingantaccen ilimi da kiwon lafiya, lamarin da ke buƙatar shugabanci nagari da manufofin da za su fifita jin daɗin jama’a.

Kwankwaso ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan da suka dace domin inganta tsaro, walwala da ci gaban ƙasa, tare da ƙarfafa ’yan Najeriya su ci gaba da neman shugabanci nagari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments