Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiAFRI-CIRD ta yabawa Majalisar Kano kan yunkurin daidaita kuɗin makarantu masu zaman...

AFRI-CIRD ta yabawa Majalisar Kano kan yunkurin daidaita kuɗin makarantu masu zaman kansu

Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gaggauta sanya hannu kan kudirin

Cibiyar African Centre for Innovative Research and Development (AFRI-CIRD) ta yabawa Majalisar Dokokin Jihar Kano kan amincewa da Kudirin Gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano na 2026.

Ta bayyana matakin a matsayin babban ci gaba wajen tabbatar da adalci da sauƙaƙa nauyin kuɗaɗen ilimi ga iyaye.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, AFRI-CIRD ta ce kudirin da majalisar ta amince da shi a ranar 4 ga Agustan 2026 ya tanadi tsarin sa ido kan kuɗaɗen makarantu masu zaman kansu, tare da iyakance karin kuɗin makaranta zuwa kaso 10 cikin 100 kacal a shekara. Haka kuma, kudirin ya haramta karɓar kuɗaɗe masu tsanani wajen gudanar da jarabawar waje.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman tanade-tanaden kudirin shi ne wajabta wa makarantu tuntubar Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) kafin yin duk wani ƙarin kuɗin makaranta.

A cewar AFRI-CIRD, akwai makarantu da dama da ba su kafa PTA ba ko kuma suka hana ƙungiyar taka rawar da ta dace, lamarin da ya hana iyaye damar shiga tattaunawar da ta shafi kuɗaɗen da ake karɓa.

Ta ce sabon kudirin ya bai wa irin waɗannan makarantu damar gyara tsarin tafiyarsu ta hanyar kafa ingantacciyar PTA, tare da gargadin cewa duk makarantar da ta ƙi bin dokar za ta fuskanci hukunci bayan kudirin ya zama doka.

AFRI-CIRD ta ƙara da cewa binciken da ta gudanar a fannin manufofin ilimi a jihohi daban-daban ya nuna cewa karin kuɗaɗen makaranta ba tare da tsari ba na sa iyaye jinkirta saka yara a makaranta ko kuma cire su daga karatu saboda rashin iya biyan kuɗin.

Ta bayyana cewa sabon tsarin zai rage wannan matsala ta hanyar tabbatar da cewa karin kuɗaɗen makaranta yana cikin ƙa’ida, rage kuɗin hukumar daga kaso 15 cikin 100 zuwa kaso biyar cikin 100, tare da dakile karin kuɗaɗen jarabawa ba bisa ka’ida ba.

Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya gaggauta sanya hannu kan kudirin domin ya fara aiki kafin sabon zangon karatu.

Haka kuma, ta buƙaci ƙungiyoyin fararen hula, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da kafafen yaɗa labarai su mara wa wannan yunƙuri baya domin tabbatar da kudirin ya zama doka cikin gaggawa.

Har ila yau, ta buƙaci gwamnati ta tabbatar da hukunta duk makarantar da ta karya dokar, tare da tabbatar da cewa shugabancin Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ya kasance bisa ƙwarewa da cancanta.

AFRI-CIRD ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta tsarin ilimi mai inganci, adalci da sauƙin biyan kuɗi ga dukkan yara a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments