Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroAna zargin an raba sama da N700m domin shirin juyin mulki

Ana zargin an raba sama da N700m domin shirin juyin mulki

Bincike ya ce an tura kuɗaɗen ga jami'an tsaro, fararen hula da malaman addini

Sabbin bayanai daga binciken jami’an tsaro sun bayyana yadda ake zargin an raba kuɗaɗen da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya bayar domin tallafa wa yunkurin juyin mulkin da aka ce ya ci tura a shekarar 2025.

Rahoton binciken ya nuna cewa ana zargin Sylva ya tura kuɗaɗen ta hanyar kamfanin Purple Waves Limited, wani kamfani da ke Abuja, kafin a miƙa su ga wani ɗan canji mai suna Abdullahi Sani Mohammed domin rabawa bisa umarnin Kanal Mohammed Ma’aji.

Takardun binciken sun nuna cewa an samu sama da N5bn a asusun kamfanin kafin a fara fitar da kuɗaɗen a watan Satumban 2025.

Tsakanin 10 zuwa 30 ga watan, an gudanar da ma’amaloli 47 inda aka tura sama da N700m zuwa ga mutane da kamfanoni daban-daban.

Masu binciken sun ce an tsara fara aiwatar da shirin ne a ranar 1 ko 4 ga Oktoban 2025, amma ya rushe bayan kama Kanal Ma’aji a ranar 29 ga Satumba.

Rahoton ya kuma ce Abdullahi Mohammed ya ci gaba da raba kuɗaɗen har bayan kama Ma’aji, yayin da Purple Waves Limited ta ci gaba da tura masa wasu kuɗaɗe har zuwa ranar 2 ga Oktoban 2025.

Binciken ya nuna cewa Abdullahi Mohammed ya karɓi jimillar N785m daga kamfanin tsakanin 20 ga Satumba zuwa 2 ga Oktoban 2025.

Masu bincike sun ce kuɗaɗen sun isa hannun jami’an soja masu aiki da masu ritaya, wasu fararen hula, kamfanoni da kuma malaman addini da aka ce an nemi su yi addu’o’i domin nasarar shirin.

Haka kuma, takardun binciken sun bayyana cewa waɗanda ake zargi da shirin sun yi amfani da kalmomin noma a matsayin lambobin sirri wajen gudanar da sadarwarsu, domin ɓoye ainihin manufar shirin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments