Ofishin Shugaban Ƙasar Iran ya musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Massoud Pezeshkian ya yi murabus, yana mai bayyana su a matsayin “ƙarya tsagwaronta.”
Mataimakin Daraktan Sadarwa da Yaɗa Labarai na Ofishin Shugaban Ƙasa, Mehdi Tabatabaei, ya ce wasu masu tsattsauran ra’ayi ne ke yaɗa irin waɗannan rahotanni domin kawo cikas ga haɗin kan ƙasar.
Rahotannin sun biyo bayan wasu kalamai da malamin addini, Mohammad Bagher Kharrazi, ya yi, inda ya yi iƙirarin cewa Mojtaba Khamenei ya ce idan Shugaba Pezeshkian ya sake miƙa takardar murabus, za a amince da ita.
Sai dai Fadar Shugaban Ƙasar Iran ta yi watsi da wannan iƙirari, tana mai jaddada cewa ba shi da tushe balle makama, tare da tabbatar da cewa babu wani murabus da shugaban ƙasar ya miƙa.