Hukumar Kwallon Kafa ta Falasdinu (PFA) ta zargi Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) da gaza aiwatar da dokokinta kan Isra’ila, tana mai cewa rashin ɗaukar mataki na tsawon shekaru ya haifar da durƙushewar harkokin ƙwallon ƙafa a Falasdinu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, PFA ta ce sama da ‘yan wasa, masu horaswa, alkalan wasa, jami’ai da mambobin ƙungiyar ƙwallon ƙafa 1,013 ne suka rasa rayukansu a yaƙin da ake yi a Gaza.
Ta kuma yi zargin cewa an lalata filayen wasa, cibiyoyin horas da ’yan wasa da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa na ƙwallon ƙafa.
Hukumar ta kuma soki FIFA kan rashin ɗaukar mataki game da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila da ke aiki a yankunan Falasdinu da aka mamaye, tana mai cewa ƙorafe-ƙorafen da ta gabatar tun fiye da shekaru 15 har yanzu ba a warware su ba.
PFA ta ce, “Shiru a lokacin da ake zargin ana aikata kisan ƙare-dangi yana nufin haɗa baki,” tana mai jaddada cewa ba za ta ci gaba da amincewa da alkawuran da ba a cika ba.
A shekarar da ta gabata, FIFA ta bayyana cewa ba za ta dakatar da Isra’ila daga shiga gasa ta ƙasa da ƙasa ba, tana mai cewa ba ita ce za ta warware rikice-rikicen siyasa ba.
Wannan matsayi ya jawo suka daga wasu magoya bayan ƙwallon ƙafa, waɗanda suka kwatanta lamarin da matakin da FIFA ta ɗauka na dakatar da Rasha daga gasa bayan mamayar Ukraine.
A halin yanzu kuma rahotanni sun nuna cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila na shirin janye goyon bayanta ga sake zaɓen shugaban FIFA, Gianni Infantino, yayin da matsin lamba ke ƙaruwa a kansa.