Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiManchester United ta kafa tarihin fara kakar Premier League mafi muni cikin...

Manchester United ta kafa tarihin fara kakar Premier League mafi muni cikin shekaru 40

Ƙungiyar Manchester United ta tashi kunnen doki 1-1 da Tottenham Hotspur, duk da cewa Tottenham ta kammala wasan da ’yan wasa 10 a fafatawar da suka yi a Old Trafford.

Ƙungiyar Manchester United ta tashi kunnen doki 1-1 da Tottenham Hotspur, duk da cewa Tottenham ta kammala wasan da ’yan wasa 10 a fafatawar da suka yi a Old Trafford.

Bryan Mbeumo ne ya fara zura wa United ƙwallo bayan ya karɓi fas ɗin Matheus Cunha, amma Dominic Solanke ya farke wa Tottenham a minti na biyu bayan cikar mintuna 90, ta hanyar bugun kai.

Tottenham ta rasa ɗan wasanta Rodrigo Bentancur bayan alkalin wasa ya ba shi jan kati bisa zargin kai wa Luke Shaw hari da kansa. Duk da haka, United ta kasa cin moriyar ƙarin ɗan wasa.

Sakamakon ya sa Manchester United ta samu maki shida kacal a wasanni shida na farko na gasar Premier League, abin da ya zama mafi munin fara kakar wasa ga ƙungiyar cikin shekaru 40, tun kakar 1986/87 da ta samu maki biyar a wasanni shida.

United tana matsayi na 12 a teburin gasar, yayin da Tottenham, wadda har yanzu ba ta yi nasara ba, ta koma matsayi na 18 bayan samun maki uku daga canjaras uku.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments