Fitar da takardun tsayawa takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 da Hukumar INEC ta yi ya sake tayar da muhawara kan bayanan karatun Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bayan an lura cewa takardun da aka wallafa sun ƙunshi shaidar digirinsa daga Chicago State University kawai, ba tare da bayanan makarantar firamare da sakandare ba.
Lamarin ya jawo martani daga lauyoyi da jam’iyyun adawa, inda wasu manyan lauyoyi suka ce kundin tsarin mulki ya tanadi cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya mallaki aƙalla shaidar kammala makarantar sakandare ko makamancinta. Wasu kuma sun bayyana cewa barin guraben takardun firamare da sakandare babu komai na iya ƙara haifar da tambayoyi daga jama’a, yayin da wasu lauyoyin suka ce hakan ba ya hana mutum cancantar tsayawa takara muddin ya cika sauran sharuddan doka.
INEC ta bayyana cewa ba aikinta ba ne tantance sahihancin takardun karatun ‘yan takara kafin wallafa su ba. Hukumar ta ce aikinta shi ne karɓar takardun da kuma wallafa su domin jama’a su duba, yayin da duk wani ƙalubale kan sahihanci ko cancantar takardu ya rage ga kotuna.
Jam’iyyun ADC da NDC sun bukaci Shugaba Tinubu ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ba a bayyana bayanan karatunsa na firamare da sakandare ba, suna cewa hakan ya sake buɗe tsohuwar muhawarar da ta biyo bayan zaɓen 2023. A gefe guda kuma, Labour Party ta ce babu wata matsala ta doka a cikin lamarin, tana mai jaddada cewa kotuna sun riga sun tabbatar da cancantar Tinubu a shari’o’in da suka biyo bayan zaɓen da ya gabata.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ministan wasanni Solomon Dalung sun yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi wa ‘yan Najeriya cikakken bayani domin kawar da duk wani shakku. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Fadar Shugaban Ƙasa da jam’iyyar APC ba su fitar da wata sanarwa kan sabon ce-ce-ku-cen ba.