Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos ta fara gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna zargin wasu jami’anta da dukan wani mai sana’ar sayar da kayan zinariya a yankin Festac.
Mutumin ya ce yana kan hanyarsa ta kai wa wani abokin ciniki sarkar wuya ne lokacin da jami’an suka tare shi suka bincike shi. Ya ce duk da cewa ba su samu wani abu da ya saba doka ba, sun ga ma’aunin da yake amfani da shi wajen auna zinariya, sannan suka zarge shi da cewa ana amfani da shi wajen auna tabar wiwi.
A cewarsa, jami’an sun umarce shi da ya bi su ofishin ‘yan sanda, amma ya ƙi saboda bai aikata wani laifi ba. Ya kuma yi zargin cewa jami’an, waɗanda ya ce ba sa sanye da cikakken kakin ’yan sanda kuma sun zo ne da wata mota marar rajista, sun yi ƙoƙarin tilasta shi shiga motarsu kafin daga bisani ɗaya daga cikinsu ya buge shi da bindiga tare da lakada masa duka.
Bayan bidiyon ya yaɗu, Rundunar ‘Yan Sandan Lagos ta bayyana cewa ta gano jami’an da ake zargi, waɗanda ke aiki a Area E Command. Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Fatai Tijani, ya umarci a gaggauta gabatar da su hedikwatar rundunar domin gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakin ladabtarwa idan an same su da laifi.
Rundunar ta kuma roƙi mutumin da ya bayyana a bidiyon da ya tuntubi Complaint Response Unit (CRU) domin taimakawa binciken, tare da tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da bincike cikin gaskiya kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka da ƙa’idojin aikin ’yan sanda suka tanada.