Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta buƙaci Masarautar Saudiyya da ta haɗa hannu da Najeriya wajen inganta tsarin ilimin Almajirai da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Oluremi Tinubu ta ce rashin bai wa Almajirai da sauran yaran da ba sa zuwa makaranta ilimin zamani na iya ƙara ta’azzara matsalolin rashin tsaro a ƙasar, tana mai jaddada cewa akwai buƙatar haɗa karatun Alƙur’ani da ilimin boko da kuma koyon sana’o’i domin inganta makomar yaran.
Ta bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen bunƙasa tsarin Almajiranci ba tare da tauye koyarwar addinin Musulunci ba, tare da samar wa yara ilimin da zai ba su damar dogaro da kansu a nan gaba.
A nasa jawabin, Jakadan Saudiyya ya ce ƙasarsa na da kyakkyawar alaƙa da Najeriya ta fuskar tarihi, addini da al’adu, yana mai bayyana shirinsu na ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa, musamman a fannin tattalin arziki da ci gaban al’umma.