Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa2027: Za mu sake mara wa Tinubu baya - Sarkin Musulmi

2027: Za mu sake mara wa Tinubu baya – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya yaba da irin ayyukan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi, yana mai cewa ya gudanar da abubuwan da ba a taɓa yi ba a Najeriya.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron ƙungiyar Fulani Makiyaya da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa:

“Ko kuna so ko ba kwa so shugaban ƙasa Tinubu ya yi abin da ba a taɓa yi ba, dan haka, dole ne mu gode masa mu kara gode masa mu sake ba shi goyon baya ya ci gaba da ayyukan da yake yi na alheri a ƙasar nan.”

Ya jaddada cewa ya kamata ‘yan Najeriya su nuna godiya tare da ci gaba da bai wa shugaban ƙasar cikakken goyon baya domin ya ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da zai amfani ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments