Haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi ‘yan sanda, sojoji da jami’an tsaron sa-kai ta dakile wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a kan hanyar Gidan Giye–Magazu da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
‘Yan sanda sun ce an gudanar da aikin ne ranar Juma’a bayan samun sahihan bayanan sirri cewa tarin ’yan bindiga dauke da makamai na ƙoƙarin tsallaka hanyar.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an Sashen Yaƙi da Manyan Laifuka (VCRU) sun isa yankin da misalin ƙarfe 12:30 na rana, inda ’yan bindigar suka yi musu kwanton ɓauna tare da buɗe musu wuta.
Sai dai jami’an tsaron sun mayar da martani da, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai tsanani. A cewarsa, an kashe ’yan bindiga da dama, yayin da wasu da dama suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga.
Rundunar ta ce motar aiki guda ɗaya ta ‘yan sanda ta samu matsala a tayoyi yayin artabun, amma hakan bai hana jami’an ci gaba da farmakin ba har suka tilasta wa ’yan bindigar janyewa da watsar da shirin harinsu.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A.M. Bello, ya yaba da jarumta da ƙwarewar jami’an tsaron, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata laifuka domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.