Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano kuma Darakta Janar na Yaɗa Labarai, Sanusi Bature D-Tofa, ya yi suka mai zafi kan tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Comrade Aminu Abdussalam, inda ya ce ba shi da magoya baya a siyasar Kano.
Sanusi Bature ya bayyana hakan ne ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya yi ikirarin cewa Aminu Abdussalam ba zai samu goyon bayan jama’a ba idan ba saboda kasancewarsa tare da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewarsa:
“Ban taɓa ganin ɗan takarar gwamna da babu jama’a a bayansa ba irin Comrade Aminu Abdussalam, kuma ba don ya fake a bayan Kwankwaso ba, da mutum biyu ne za su dinga binsa a baya.”
Kalaman Sanusi Bature na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun muhawara da rikice-rikicen siyasa a Jihar Kano, musamman tsakanin gwamnatin da ta balle daga Kwankwasiyya da wasu daga cikin yan NDC.