Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Adamu Ibrahim Bakori, ya ce masu gangamin ‘Tinubu Must Go’ suna da ’yancin gudanar da taro ba tare da sanar da ’yan sanda ba, sai dai ya bayyana cewa sanar da jami’an tsaro na taimakawa wajen tabbatar da tsaro ga masu taron da sauran jama’a.
Kwamishinan ya ce ya tuntubi jagoran ƙungiyar, Barrister Abba Hikima, bayan ya ga sanarwar taron a kafafen sada zumunta, inda ya ba shi shawarar ɗage taron domin su tattauna kan lamarin.
Sai dai a safiyar Lahadin nan, Abba Hikima da magoya bayan ƙungiyar sun isa wurin da aka shirya gudanar da gangamin, amma jami’an ’yan sanda suka hana su gudanar da shi.
A wani faifan bidiyo, Abba Hikima da magoya bayan ƙungiyar sun yi kira ga Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya da kwamishinan ’yan sandan jihar da su sake duba matsayarsu kan lamarin.
Sun kuma zargi jami’an tsaro da nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu, zargin da ba a samu martanin rundunar a kansa cikin bayanan da aka bayar ba.