Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNDLEA ta cafke ’yar Afirka ta Kudu da hodar iblis a filin...

NDLEA ta cafke ’yar Afirka ta Kudu da hodar iblis a filin jirgin Abuja

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa NDLEA ta kama wata ’yar ƙasar Afirka ta Kudu mai suna Will Ann, mai shekaru 38, bisa zargin shigo da kilo 5.75 na hodar iblis ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A lokacin da aka kama ta, tana tare da ɗanta mai shekaru uku.

A cewar NDLEA, an gano miyagun ƙwayoyin ne a cikin akwatuna biyu da matar ta fara musanta cewa nata ne.

Sai dai bayan gudanar da bincike da ya nuna bayanan jakunkunan sun yi daidai da na fasfo ɗinta, ta amince cewa kayan mallakinta ne.

Hukumar ta bayyana cewa tana zargin matar na da alaƙa da wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa, kuma ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ake zargi da hannu a lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments