Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDangote ya sanya ladan duba N500,00 ga masu tona asirin amfani da...

Dangote ya sanya ladan duba N500,00 ga masu tona asirin amfani da motocinsa ba bisa ƙa’ida ba

Kamfanin Dangote ya ƙaddamar da wani sabon shiri na yaƙi da amfani da manyan motocinsa wajen ayyukan da suka saɓa wa ƙa’ida.

Kamfanin ya bayyana cewa duk wanda ya bayar da sahihin bayani da zai kai ga gano irin waɗannan laifuka zai samu kyautar kuɗi har ta ₦500,000.

A cewar kamfanin, an samu wasu direbobi da ke amfani da manyan motocin Dangote wajen jigilar mutane ko wasu kayayyaki ba tare da izini ba domin samun kuɗi.

Saboda haka, an ƙaddamar da wannan tsari ne domin dakile irin waɗannan ayyuka da kuma kare mutuncin kamfanin.

Dangote ya bayyana cewa kowace mota tana da aikin da aka ware mata.

Motocin siminti za su ɗauki siminti da wasu sinadarai da aka amince da su kawai, motocin sukari za su ɗauki sukari kaɗai, yayin da sauran motocin kamfanin kamar na NASCON, matatar mai da na taki su ma za su yi jigilar kayayyakin da aka ware musu kawai.

Kamfanin ya buƙaci masu ba da rahoto su aika da bayanai kamar nau’in mota, lambar mota, launinta, wurin da aka gan ta da kuma irin kayan da take ɗauke da su.

Haka kuma, idan akwai dama, a ɗauki hoto domin sauƙaƙa binciken da za a gudanar.

Dangote ya ce duk bayanin da aka tabbatar da sahihancinsa kuma ya taimaka wajen cafke masu amfani da motocin kamfanin ba bisa ƙa’ida ba zai bai wa wanda ya bayar da bayanin ladan ₦500,000.

Kamfanin ya kuma ce yana aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da bin doka da kare kadarorinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments