Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiAtiku ya kalubalanci shirin ƙara kuɗin WAEC da NECO

Atiku ya kalubalanci shirin ƙara kuɗin WAEC da NECO

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da shirin da ake cewa Gwamnatin Tarayya na son aiwatarwa na ƙara kuɗin rubuta jarabawar WAEC da NECO zuwa Naira 50,000 daga shekarar 2027.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa irin wannan mataki zai ƙara jefa iyaye cikin matsin tattalin arziki, musamman a wannan lokaci da tsadar rayuwa ke ƙara tsananta a faɗin ƙasar.

Ya ce idan aka aiwatar da ƙarin kuɗin, ɗalibai da dama daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi na iya rasa damar rubuta jarabawar kammala sakandare, lamarin da zai ƙara yawan yaran da ke barin makaranta da kuma rage damar samun ilimi mai zurfi.

Atiku ya buƙaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta mayar da hankali wajen bunƙasa fannin ilimi ta hanyar ƙara saka hannun jari, inganta makarantu da ɗaukar malamai, maimakon ɗora wa iyaye ƙarin nauyin kuɗaɗen karatu da jarabawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments