Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan kasuwar man fetur da su gaggauta rage farashin litar fetur domin ya dace da saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya zuwa ƙasa da Dala 70 kan ganga.
Gwamnatin ta ce babu wani dalili da zai sa a ci gaba da sayar da fetur a farashin da ake sayarwa a halin yanzu, idan aka yi la’akari da yadda farashin ɗanyen mai ya ragu a kasuwannin duniya.
Heineken Lokpobiri, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar domin tattauna yadda ya kamata farashin man fetur ya kasance.
Ya jaddada cewa farashin fetur ya kamata ya riƙa daidaituwa da yanayin kasuwar duniya, musamman idan aka samu sauyin farashin ɗanyen mai, domin tabbatar da adalci ga masu amfani da man fetur.
Kalaman ministan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sa ido kan sauye-sauyen farashin man fetur a Najeriya, yayin da jama’a ke fatan ganin raguwar farashin idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da sauka.