Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƊan Majalisa ya roƙi Tinubu ya dakatar da sauye-sauyen da ake shirin...

Ɗan Majalisa ya roƙi Tinubu ya dakatar da sauye-sauyen da ake shirin yi wa NYSC

Wani ɗan Majalisar Wakilai, Philip Agbese, ya buƙaci Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da aiwatar da sabbin sauye-sauyen da ya amince da su kan shirin bautar ƙasa na NYSC.

Agbese ya yi gargadin cewa wasu daga cikin sauye-sauyen da aka gabatar na iya raunana ainihin manufar shirin, wadda ta haɗa da ƙarfafa haɗin kan ƙasa, bunƙasa zaman tare tsakanin al’ummomi, da kuma tallafa wa tsaron ƙasa.

Ɗan majalisar, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Ado/Okpokwu/Ogbadibo a Benue, kuma mamba ne a kwamitocin Majalisar Wakilai masu kula da harkokin matasa da tsaro, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce duk wani sauyi da za a yi wa shirin NYSC ya kamata ya kasance bayan cikakken nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da cewa ba zai kawo cikas ga manufofin da aka kafa shirin domin cimmawa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments