’Yan bindiga sun kai mummunan hari ƙauyen Kuda-Kuda da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, inda suka kashe babban limamin ƙauyen, Liman Audu, tare da wasu mutum uku.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma yi awon gaba da mutum shida bayan sun shafe kusan sa’o’i biyu suna harbe-harbe tare da sace dabbobi da haddasa firgici a yankin.
Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun rika shiga gida-gida suna kwasar mutane, yayin da wasu suka rasa rayukansu saboda ƙin bin maharan zuwa daji.
An ce wannan shi ne hari na 11 da aka kai wa ƙauyen, yayin da har yanzu hukumomin jihar ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.