Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta musanta wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke zargin wani jami’in ɗan sanda da hulɗa da ‘yan ta’adda a Jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa mutanen da aka gani a bidiyon ba ‘yan ta’adda ba ne, illa mambobin Vigilante Group of Nigeria (VGN) da kuma mafarauta da aka yi wa rajista, waɗanda ke aiki tare da jami’an tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.
‘Yan sandan sun ce bidiyon ya nuna wata ganawa ce ta yau da kullum tsakanin jami’in ɗan sanda da masu sa kai kafin su tafi gudanar da aikin tsaro, kuma duk wata magana da ke cewa suna hulɗa da ‘yan ta’adda ƙarya ce da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotannin ƙarya, tare da dogaro da bayanan da hukumomin tsaro ke fitarwa a hukumance. Ta kuma yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin doka kan duk wanda aka samu yana yaɗa labaran ƙarya da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da ayyukan tsaro.