Saturday, October 17, 2026
HomeLafiyaAmurka ta samar da allurar rigakafin cutar Ebola

Amurka ta samar da allurar rigakafin cutar Ebola

Jami’an lafiya na Amurka sun sanar da samar da wata allurar rigakafin cutar Ebola ta gwaji, yayin da ake ci gaba da fuskantar yaɗuwar cutar a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa an fara jigilar maganin daga Amurka domin gudanar da gwaje-gwajen asibiti.

An ce an ƙera maganin ne ta amfani da sanadaran garkuwar jiki daga mutanen da suka kamu da cutar Ebola kuma suka warke a baya.

Bayan kammala shirye-shiryen farko, WHO za ta gudanar da ƙarin gwaje-gwaje don tabbatar da inganci da amincinsa.

A halin yanzu dai, babu wani magani ko allurar rigakafi da aka amince da ita gaba ɗaya domin magance nau’in cutar Ebola na Bundibugyo, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da kamuwa da sama da mutum 1,000.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments