Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro‘Yan sanda sun tabbatar da fashewar bam a Kasuwar Mushin da ke...

‘Yan sanda sun tabbatar da fashewar bam a Kasuwar Mushin da ke Legas

Fashewar Bam Ta Girgiza Kasuwar Mushin a Jihar Legas

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Fatai Tijani, ya tabbatar da faruwar fashewar bam a Kasuwar Kayayyakin Takalma da ke Mushin, yana mai cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin kuma yankin ya koma cikin kwanciyar hankali.

A cewarsa, bayan samun rahoton fashewar, rundunar ta gaggauta tura jami’an EOD (Explosive Ordnance Disposal) domin killace wurin da kuma gudanar da bincike.

Binciken farko ya nuna cewa an dasa bam ɗin ne a ƙarƙashin wata mota, a gefen kujerar fasinja, kuma ya fashe ne lokacin da aka kunna injin motar.

Kwamishinan ya ce mutum guda ne ya samu rauni a lamarin, kuma an garzaya da shi asibiti inda ake kula da lafiyarsa.

Ya kuma tabbatar da cewa bayan cikakken binciken da aka gudanar, ba a gano wani ƙarin bam a yankin ba, yayin da aka tattara ragowar bam ɗin domin ci gaba da binciken kwakwaf.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments