Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroSojoji sun kashe ‘yan ta’adda 2, tare da kwato makamai a katsina

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 2, tare da kwato makamai a katsina

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda biyu tare da ƙwato manyan makamai da kayayyaki a samamen da suka kai maboyarsu a jihar Katsina.

Dakarun Brigade 17 na rundunar sojin Najeriya da ke gudanar da aikin Operation Clean Sweep III sun kashe mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a wani samame da suka kai a ƙauyen Ginchawa da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce an gudanar da farmakin ne a ranar 21 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri kan maboyar ‘yan ta’adda a yankin.

A yayin harin, ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin mayar da martani, sai dai dakarun sojojin sun yi nasarar murƙushe su da ƙarfin wuta, lamarin da ya tilasta sauran tserewa zuwa cikin daji.

Bayan kammala samamen, sojojin sun ƙwato bindigogi kirar PKT guda biyu, bindigar gargajiya guda ɗaya, rumbun harsasai na AK-47, harsasai 75 kirar 7.62mm NATO, babura uku, wayoyin salula biyu, na’urar sadarwa ta Motorola, kayan sojoji, da kuma shanu biyu da awaki huɗu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa babu wani soja da ya rasa ransa ko ya ji rauni a yayin aikin, yayin da ake kyautata zaton wasu daga cikin ‘yan ta’addan da suka tsere sun samu raunukan harbin bindiga, sakamakon alamun jini da aka gano a maboyarsu da hanyoyin tserewarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments