Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta sake bayyana goyon bayanta ga kafa rundunar ’yan sandan jihohi, tana mai cewa hakan ya dace da tsarin gwamnatin tarayya da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.
Gwamnonin sun bayyana matsayarsu ne bayan taron da suka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
A cewarsu, kafa ‘yan sandan jihohi na daga cikin matakan da za su taimaka wajen inganta tsaro a matakin jihohi tare da ba kowace jiha damar taka rawar gani wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sun kuma bayyana cewa kwamishinonin shari’a na jihohi za su yi nazari kan gyare-gyaren kundin tsarin mulkin da ake bukata domin tabbatar da kafa rundunar ’yansandan jihohi cikin tsarin doka.