Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gudanar da wata ganawa da manyan sarakunan gargajiya na jihar domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar al’ummar yankin.
Taron ya samu halartar Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, da hakimai da dakatai daga sassa daban-daban na jihar.
An shirya ganawar ne da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya wajen samar da ingantaccen tsaro, zaman lafiya da ci gaban jihar.